23 Satumba 2014 - 08:46
Amurka Ba Da Gaske Take Ba A Yaki Da 'Yan Ta'addar ISIS

Ministan harakokin wajen Siriya ya ce Amurka ba da gaske ta ke ba wajen yaki da 'yan ta'adda. Yayin da yake hira da tashar telbijin ta Rusiya Alyaum, Walid Mu'alim ya ce inda kasar Amurka da gaske take wajen yaki da kungiyar 'yan ta'addar Da'esh ko ISIS da kuma wasu kungiyoyin ta'adda na daban, da ta bi lamarin ta hanyar MDD ,da kuma ba ta ware wasu kasashe ba kamar kasashen Rasha, Iran da kuma Siriya.

Mu'alim ya ce firicin Amurka na cewa ba za ta hada kai ba da Gwamnatin Siriya wajen yakar 'yan ta'addar ISIS sai dai da wasu kungiyoyin 'yan tawayen Siriya irinsu jabhatu Nusra, abu ne da zai sanya shakku ga wani mai hankali alhali har yanzu wadannan kungiyoyi da Amurka ta ce za ta hada kai da su na zubar da jinin fararen hula a kasar ta Siriya.

 

Ministan ya kara da cewa idan ana so a cimma gurin da aka sanya a gaba na yaki da ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya, to wajibi ne a girmama kasashen yakin, kuma duk wani mataki da ake son dauka na yaki da ta'addancin to wajibi ne a dauki shi a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya. ABNA